Majalisa ba zata lamunci kin amfani da na’urar tantance katin zabe ba - Dogara

Majalisa ba zata lamunci kin amfani da na’urar tantance katin zabe ba - Dogara

Kakakin majalisar wakilai, Hon Yakubu Dogara, ya sha alwashin cewa ýan majalisa tarayya za su dakile duk wani yunkuri na ci gaba da kawo tsaiko a gyaran dokar zabe, musamman amfani da na’urar tantance katin zabe a zaben 2019.

Da yake bayyana ynkurin a matsayin kokarin ganin an sake samun nasarar kamar na zaben 2015, Dogara yace gabatar da dogar zai magance tsoron cewa wasu na son magudi a zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a jawabin maraba da dawowa daga dogon hutun da majalisar ta tafi.

Majalisa ba zata lamunci kin amfani da na’urar tantance katin zabe ba - Dogara

Majalisa ba zata lamunci kin amfani da na’urar tantance katin zabe ba - Dogara

Ya ba mutane tabbacin cewa da zaran majalisa ta kama aiki sosai za’a duba dokar gyaren zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Ahmed Gumi, Matthew Kukah, Bishap Oyedepo sun karasa gidan Obasanjo domin ganawarsu da Atiku (Hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa majalisar dattawa ta amince da naira biliyan 234.51 na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Kudin da aka amince da shi ya samu ragin naira biliyan 7.9 cikin naira biliyan 242.45 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Majalisar sun kuma amince da mayar da naira biliyan 189 na zaben 2019 zuwa shirye-shirye na musamman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel