Ministocin Najeriya da su ka gaza samun tikin takarar Gwamnan Jihohin su

Ministocin Najeriya da su ka gaza samun tikin takarar Gwamnan Jihohin su

Yayin da aka dawo bakin aiki musamman bayan zabukan da Jam’iyyu su kayi na tsaida ‘Yan takarar su a zabe mai zuwa. Mun kawo maku jerin Ministocin da su ka nemi takara su ka fadi kuma yanzu za su koma kujerun su ko su ka bar Jam'iyyar.

Ministocin Najeriya da su ka gaza samun tikin takarar Gwamnan Jihohin su

Wasu Ministoci ba su yi nasara wajen samun tikitin takara a Jam’iyyar APC ba

1. Adebayor Shittu

APC ta hana Ministan sadarwan Najeriya neman takarar Gwamna Jihar Oyo. Ta tabbata dai cewa Shittu bai yi wa kasa bauta ba watau NYSC a sa’ilin da ya kammala karatun Jami’a inda ya tsunduma cikin siyasa kai-tsaye.

2. Mama Taraba

Haka-zalika tun kafin a kai ko ina, APC ta hana Aisha Jummai Alhassan takara wanda wannan abu yayi mata ciwo har ya sa Mama Taraba tayi murabus, ta kuma fice daga APC ta koma UDP inda ta ke neman Gwamna.

KU KARANTA: Don a bata mani suna Gwamnatin Buhari ta tsiri bincike na – Sanata

3. Mustapha Baba Shehuri,

Karamin Ministan lantarki da kuma na gidaje da ayyuka na Najeriya Baba Shehuri ya nemi takarar Gwamna a Jihar Borno amma ya sha kasa. Tsohon ‘Dan Majalisar ya fadi zaben fitar da gwani ne a hannun Babagana Umara-Zulum.

4. Mansur Dan Ali

Minsitan tsaro na Najeriya Janar M. Dan Ali mai ritaya yana cikin wadanda su ka sha kasa a Jihar Zamfara wajen neman Gwamna. Ko da dai har yanzu ana cikin rudani a Jihar, sai dai ba mamaki Mukhtar Shehu Idris ya zama ‘Dan takarar APC.

5. Usani Usani

Ana tsakar murna cewa Ministan Neja-Delta Usani Usani Uguru zai yi takarar Gwamna a Jihar Kuros Riba a APC ne kurum sai aka ji cewa wani bangaren APC a Jihar ta tsaida Jon Enoh a matsayin ‘Dan takara ta zauna a haka inji Uwar Jam'iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel