Kotu ta tabbatar da Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan Imo karkashin APC

Kotu ta tabbatar da Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan Imo karkashin APC

- Kotu ta tabbatar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin dan takarar kujerar gwamnan jihar Imo karkashin jam'iyyar APC

- Kotun ta kuma haramtawa hukumar INEC karbar sunan wani dan takarar karkashin jam'iyyar APC in har ba Uzodinma ba

- Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC na rade-radin sake gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamnan jihar Imo

Wata babbar kotu da ke birnin tarayya Abuja ta tabbatar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan jihar Imo a zaben 2019 karkashin jam'iyyar APC.

Kotun wacce ta yanke wannan hukunci karkashin shugabancin mai shari'a O. A. Musa ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, zata dauki Udinma kadai a matsayin dan takarar gwamnan jihar Imo a babban zabe na 2019.

Mai shari'a O. A. Musa wanda ya bayar da wannan umurnin a ranar Talata, ya kuma haramtawa INEC wallafa "sunan wani dan takara inba Sanata Hope Uzodimma na jam'iyyar APC ba, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Imo a zaben 2019 da ke gabatowa" duba da irin kararraki makamantan wannan da ke gaban alkalai.

KARANTA WANNAN: Yar takarar shugaban kasa Ezekwesili ta roki 'yan Nigeria su hada mata kudin yakin zabe

Kotu ta tabbatar da Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan Imo karkashin APC

Kotu ta tabbatar da Uzodinma a matsayin dan takarar gwamnan Imo karkashin APC

Uzodinma ta hannun lauyansa, Joe Agi (SAN) sun gabata a gaban kotun ne inda suka bukaci kotun da ta dakatar da jam'iyyar APC daga sake gudanar da wani zaben fitar da gwani na kujerar gwamnan jihar ta Imo da kuma haramtawa INEC na sake karbar sakamakon wani zaben da APC ke yunkurin yi karo na biyu a jihar.

Haka zalika daga cikin bukatun da Sanata Hope Uzodimma ya gabatar sun hada da bukatar kotun na baiwa jam'iyyar APC umurnin gabatarwa hukumar INEC sunansa a matsayin dan takarar gwamnan jihar Imo a zaben 2019 da ke gabatowa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel