Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

Majalisar dattawa ta amince da naira biliyan 234.51 na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Kudin da aka amince da shi ya samu ragin naira biliyan 7.9 cikin naira biliyan 242.45 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Majalisar sun kuma amince da mayar da naira biliyan 189 na zaben 2019 zuwa shirye-shirye na musamman.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

A cewar bukatar shugaban kasar, daga cikin kudaden ne za’a ba hukumomin tsaro kan zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun saki dan majalisa bayan majalisar ta sanya baki

Bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika zuwa ga shugaban majalisar dattawan, Dr Bukola Saraki a ranar 11 ga watan Yuli dauke da sanya hannun Buhari.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa mai taimakon shugaban kasa, Ita Enang, yace kwamitin majalisar dattawa akan harkokin zabe basu da ikon fadin inda za'a nemo kudin zaben 2019.

Mista Enang, hadimin shugaban kasa na musamman akan harkokin majalisar dattawa ya sanar da ofishin dillancin labarai a zauren su dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel