Yanzu Yanzu: Yan sanda sun saki dan majalisa bayan majalisar ta sanya baki

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun saki dan majalisa bayan majalisar ta sanya baki

- Hukumar yan sanda ta saki Abubakar Lado

- Hakan ya biyo bayan sanya baki da majalisar wakilai tayi

- Majalisar tayi barazanar aika sammaci ga sufeton janar na yan sanda idan ba'a sake shi ba

Rundunar yan sanda ta saki wani mamba na majalisar wakilai, Mista Abubakar Lado dake tsare.

An saki Lado wanda ya shafe kwanaki uku a hannun rundunar yan sandan dake yaki da fashi da makami a Abuja a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba bayan majalisar ta yi umurnin sakin shi cikin gaggawa.

Majalisar tayi barazanar aika sammaci ga sufeton janar na yan sanda, Mista Ibrahim Idris idan yan sandan suka ki sakin Lado kafin tsakar daren ranar Laraba.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun saki dan majalisa bayan majalisar ta sanya baki

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun saki dan majalisa bayan majalisar ta sanya baki

An saki Lado sannan ya koma gidansa a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Kanin Aisha Buhari ya caccaki Bindow, yace iliminsa bai isa ace ya zama gwamna ba

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan, Mista Femi Gbajabiamila wanda ya bukaci aika sammaci ga IGP, ya nemi a share zancen.

Lado ya mika godiya ga abokan aikinsa da suka kai masa doki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel