Yar takarar shugaban kasa Ezekwesili ta roki 'yan Nigeria su hada mata kudin yakin zabe

Yar takarar shugaban kasa Ezekwesili ta roki 'yan Nigeria su hada mata kudin yakin zabe

- Obiageli Ezekwesili, ta roki 'yan Nigeria su tallafa mata da kudaden da zata gudanar da yakin zabe a kokarinta na zama shugaban kasa

- Ta wallafa bayanan asusun bankinta, ta inda 'yan Nigeria za su tura mata da gudunmowarsu da zata gudanar da yakin zaben nata

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yar takarar shugaban kasar na bukatar wadannan kudaden ne a cikin kwanaki 5

A jiya Laraba, tsohuwar ministar ilimi, Obiageli Ezekwesili, ta roki 'yan Nigeria musamman wadanda za su jefa kuri'a a zaben 2019, da su tallafa mata da kudaden da zata gudanar da yakin zabe mai zuwa a kokarinta na zama shugaban kasar gobe.

Ezekwesili, wacce ta kirkiri kungiyar nan ta 'A dawo mana da 'yan matanmu' (BBOG), da ke fafutukar ganin an maido da 'yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace, ta bayyana cewa, kudaden tallafin, zasu taimaka mata wajen cimma burinta na shugabantar kasar, tare da tsara ayyukan ci gaba da zasu kai kasar Nigeria ga tudun mun tsira.

Ta wallafa wannan rokon tallafin ne a shafinta na 'Twitter' inda ta sanya bayanan asusun bankinta, ta inda 'yan Nigeria za su tura mata da gudunmowarsu ta kudin da zata gudanar da yakin zaben nata.

KARANTA WANNAN: PDP: Fito na fito da APC ta yi da Atiku ta hanyar yi masa kazafi alama ce ta shan kasa

Yar takarar shugaban kasa Ezekwesili ta roki 'yan Nigeria su hada mata kudin yakin zabe

Yar takarar shugaban kasa Ezekwesili ta roki 'yan Nigeria su hada mata kudin yakin zabe

Rahotanni sun bayyana cewa 'yar takarar shugaban kasar na bukatar wadannan kudaden ne a cikin kwanaki 5, kuma za a yi amfani da kudin wajan yakin nemo masu kad'a kuri'a da zasu zabeta, su kasa su tsare don ganin ta samu nasara a zaben 2019.

Haka zalika ta bayyana cewa bayar da gudunmowar jama'a zai aika da babban sako ga kafatanin 'yan Nigeria na nuna cewar a shirye suke su hada kudade don ceto kasarsu daga bata garin 'yan siyasa, shugabancin kama karya, kashe kashe, talauci, rashin aikin yi, kuncin rayuwa da kuma rashin sanin makomar 'yan Nigeria.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel