2019: Dalilan da yasa har yanzu Atiku bai zabi mataimakinsa ba

2019: Dalilan da yasa har yanzu Atiku bai zabi mataimakinsa ba

- A halin yanzu mutane sun sa ido domin ganin wanda Atiku zai zaba a matsayin mataimakinsa

- Al'ummar yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma duk sun huro wuta suna neman a zabi mataimakin daga yankinsu

- Akwai yiwuwar Buhari zai canja mataimakinsa hakan yasa Atiku ke jinkirtawa kafin ya zabo mataimakinsa

Tun bayan nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi na samun tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, idan masu nazarin al'ummar siyasa da mutane ya koma kan wanda zai zaba a matsayin mataimakinsa.

Daya daga cikin dalilan da yasa har yanzu Atiku bai sanar da mataimakinsa da za suyi takara ba shine akwai yiwuwar shugaba Muhammadu Buhari zai iya zabo mataimakinsa daga yankin Kudu maso Gabas ko Kudu maso Yamma na Najeriya.

Dalilan da yasa Atiku bai zabi mataimakinsa ba

Dalilan da yasa Atiku bai zabi mataimakinsa ba

Duk da cewa wata majiya daga kungiyan yankin neman zaben Atiku ta tabbatarwa Guardian cewar har yanzu bai zabi mataimakinsa ba, an gano cewar an fara mika masa sunayen wasu mutane da ake tsamanin zai zaba daya daga cikinsu.

DUBA WANNAN: Atiku zai kaiwa Obasanjo ziyara a yau

Idan ba'a manta ba cikin 'yan kwanakin nan, tsohon mai gidan Atiku, Olusegun Obasanjo ya taso da batun yiwuwar samun shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas a 2019. Wata majiya a jam'iyyar PDP ta ce Obasanjo ya bukaci a zabi mataimakin takara daga Kudu har ma ya ambaci sunan Mazi Osita Chidoka.

Amma bayan Obasanjo ya ambaci sunan Mazi Osita Chidoka, wasu jiga-jigan na jam'iyyar PDP sun karkata cewar ya dace a nemo gogagen dan boko ne domin ya yi takara tare da Atiku a shekarar na 2019.

Wasu daga cikin sunayen da aka ambata sun hada da Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Farfesa Chukwuma Charles Soludu da Farfesa Barth Nnaji da kuma tsohon gwamnan jihar Anambra Mr. Peter Obi.

A bangare guda kuma mutanen yankin Kudu maso Yamma sun huro wuta inda suke bukatar Atiku ya zabi mataimakinsa daga yankinsu musamman idan a kayi la'akari da cewar yankin ta rasa damar fitar da shugaban jam'iyya a zaben kasa na PDP da aka gudanar a Disambar wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel