PDP: Fito na fito da APC ta yi da Atiku ta hanyar yi masa kazafi alama ce ta shan kasa

PDP: Fito na fito da APC ta yi da Atiku ta hanyar yi masa kazafi alama ce ta shan kasa

- PDP ta ce fito na fito da APC ta ke yi don bata sunan Atiku Abubakar alama ce kawai ta shan kaye a zaben 2019

- Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa APC da fadar shugaban kasa sun dauki hayar yan yanar gizo don yada labaran karya da kazafi akan Atiku

- Haka zalika PDP ta ce ba a taba samun Atiku da cin hanci ba, illama dai zarge zargen da ake yiwa shugaban kasa Buhari na wawure kusan $25bn

A ranar Laraba ne jam'iyyar PDP ta ce fito na fito da ministan watsa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya yi kai tsaye, da kuma buga kugen yaki da jami'an jam'iyyar APC dama wasu jigogi a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan dan takarar shugaban kasarta, Alhaji Atiku Abubakar, alama ce da ke nuna cin galaba.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, a cikin wata sanarwa ya ce duba da sahihancin zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasar da jam'iyyar ta gudanar wanda ya baiwa Atiku Abubakar nasara, fadar shugaba Buhari dama jam'iyyar APC sun zamo cikin rudani da kokonto makomarsu a 2019, wanda ya hadda masu fara yarfe a yada jita jita.

"PDP na sane da irin fito na fito da wasu jami'an fadar shugaban kasa suka yi, sun tara marubuta da masu fasa kwabrin yanar gizo ta hanyar basu biliyoyin nairori, wanda suka dauka daga lalitar kasarmu, kawai don yada jita-jita, farfaganda maras tushe da kuma yin yarfe ga dan takarar shugaban kasarmu," a cewar jagorar jam'iyyun adawa na kasar.

PDP: Fito na fito da APC ta yi da Atiku ta hanyar yi masa kazafi alama ce ta shan kasa

PDP: Fito na fito da APC ta yi da Atiku ta hanyar yi masa kazafi alama ce ta shan kasa

KARANTA WANNAN: Zanga zangar 'yan Shi'a a Abuja: Sun bukaci 'yan Nigeria su maida Buhari Daura a 2019

"A yanzu dai ta fito fili kan tsoron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke yi na karawa da sanannen dan takara a zabe na gaba saboda rashin kwarewar iya shugabanci, wanda yasa ma yan Nigeria ke zuci zucin canja shi, wannan ne yasa suka dauki kudirin bata sunan Atiku, wanda hakan yakin tsoro ne.

"Akul, Shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC a wannan yunkurin nasu, su karkatar da dukiyar da aka tara ta hanyar jibin goshi, saboda bata sunan Atiku. Shugaban kasa Buhari ya gaza tafiyar da mulkinsa wajen farfado da tattalin arzikin kasar, hakan kuwa ba yana nufin kowa ma hakan zai yi ba."

KARANTA WANNAN: Bincike: Citta, Kanwa da Zuma na magance matsalar radadi da yawan zubar jinin al'ada ga mata

Jam'iyyar PDP ta ce Atiku bai taba fuskantar wata tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa ba, amma yanzu shugaban kasa Buhari na fara samun zarge zarge kan wawushe dukiyar kasa a gwamnatinsa, wanda kuma ya kasa kare kansa akan wadannan zarge zarge da ake masa.

PDP ta ce tunda dai Lai Mohammed na magana kan karnin cin hanci na baya, to ya kamata ya dago da maganar sace zambar miliyan 9 ($25bn) wanda aka wawushesu ta bangaren kwangilar man fetur a kamfanin NNPC da kuma ma'aikatar man fetur, karkashin gwamnatin Buhari.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel