Hadiman wani gwamnan PDP na shirin kwance masa zani a kasuwa

Hadiman wani gwamnan PDP na shirin kwance masa zani a kasuwa

Tsohon mai bawa gwamnan jihar Akwa Ibom Shawara a kan harkokin zabe, Mfon Udeme, ya bayyana cewar kaso mai yawa na hadiman gwamnan sun kammala shirin ajiye mukamansu.

Da yake magana da manema labarai a Uyo, Udeme ya bayyana cewar ajiye mukaman da hadiman gwamnan za su yi, zai shafi yankunan da yake da yawan magoya baya.

Hadiman wani gwamnan PDP na shirin kwance masa zani a kasuwa

Hadiman wani gwamnan PDP na shirin kwance masa zani a kasuwa

DUBA WANNAN: Majalisa ta nada sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

"Nan da wasu 'yan watanni gidan gwamnati zai koma tamkar kango domin fiye da kashi 80% na hadimansa sun kammala shirin ajiye mukamansu tare da yin sallama da gwamna Udom Emmanuel da gwamnatinsa," a cewar Udeme.

Sannan ya cigaba da cewa, "dole hadimansa su ke barinsa saboda ba ya girmama su kuma ga shi ba ya kaunar yin aiki da jama'a zasu amfana.

"Tsayar da Obong Nsima a matsayin dan takarar gwamna a APC, ya isa Udom sanin cewar gwamnatinsa ta zo karshe, lokacin tafiyar sa ya zo," a kalaman Udeme.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel