Na bayyana duk kadarorin da na ke da su tas a gaban Hukuma - Ekweremadu

Na bayyana duk kadarorin da na ke da su tas a gaban Hukuma - Ekweremadu

Mun samu labari cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya maidawa Gwamnatin Tarayya martani game da zargin da ake masa na cewa ya ki bayyana kadarorin sa.

Na bayyana duk kadarorin da na ke da su tas a gaban Hukuma - Ekweremadu

Ekweremadu yace akwai ban dariya a lamarin Gwamnatin Buhari

Ike Ekweremadu yayi Allah-wadai da karar da Gwamnatin Shugaba Buhari ta maka shi a gaban Kotu inda ake zargin sa da cewa bai bayyana adadin kadarorin da ya mallaka ba kamar yadda tsarin mulki da dokar kasar nan su ka tanada.

Kwamitin da aka nada domin karbo kadarorin da aka mallaka ta hanyoyin da ba su dace ba watau SPIP ta taso Ike Ekweremadu a gaba ta hannun Shugaban ta Ofem Obono-Obla. Sanatan yace wannan yunkuri ne na bata masa suna.

KU KARANTA: Ana tunani Ekweremadu zai zama 'Dan takaran kujeran Mataimakin shugaban kasa

Sanata Ike Ekweremadu ya nuna cewa babu kanshin gaskiya a binciken inda ya zargi kwamitin da neman ci masa mutunci. Sanatan na PDP yace bai aikata wani laifi ba domin kuwa ya bayyana kadarorin sa a lokacin da zai shiga ofis.

Sanatan ya tabbatar da cewa ya bayyanawa Hukumar CCB wanda nauyin bibiyar kadarorin Ma’aikatan Gwamnati ya rataya a kan ta dukkanin abin da ya mallaka shekaru 4 da su ka wuce don haka babu dalilin taso sa a gaba a wannan marra.

Mataimakin na Bukola Saraki yace babu wani dalili da zai sa kwamitin SPIP ta kawo maa wasu fam ya sake cikewa domin kuwa hakan ya sabawa ka’ida da dokar kasa ya kuma nemi Ministan shari’a ya guji aikata abin da bai dace ba ta ofishin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel