Gwamna Amosun ya yi barazanar barin APC kan zaben fidda gwani

Gwamna Amosun ya yi barazanar barin APC kan zaben fidda gwani

Gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibukunle Amosun, yayi barazanar ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan har kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka gaza marawa dan takarar gwamnansa, Abdul-Kabir Adekunle Akinlade baya.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnoni biyar da suka hada da Akinwunmi Ambode, Rochas Okorocha, Umar Ganduje, Mohammed Abubakar da Kashim Shettima sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka nemi ya sanya baki a rikicin zaben fidda gwani da ya billo a jamiyyar.

Amosun yayi barazanar ne a lokacin ganawa da wasu shugabannin jam’iyyar a fadin kananan hukumomin 20 na jihar wanda aka gudanar a gidansa dake Ibara GRA, Abeokuta.

Gwamna Amosun ya yi barazzanar barin APC kan zaben fidda gwani

Gwamna Amosun ya yi barazzanar barin APC kan zaben fidda gwani
Source: UGC

A cewar wata majiya da ta hallara a taron, tace gwamnan wanda ya sanar da magoya bayansa sakamakon ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban APC na kasa bai sanar da jam’iyyar da zai koma ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC na neman a tsige Oshiomhole

Gwamnan ya kuma caccaki wadanda ya kira da sunan masu alaka da APC ta Abuja da suka bayyana Abiodun a matsayin dan takarar gwamna maimakon Akinlade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel