Gwamnonin APC na neman a tsige Oshiomhole

Gwamnonin APC na neman a tsige Oshiomhole

- Wasu gwamnonin APC sun yi kira ga tsige shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole

- A cewar wani minista gwamnonin basu aminta da tsarin shugabancinsa ba

- Yace tuni suka tuntubi shugaba Buhari don sanin yadda za'a tsige shi

Wasu gwamnoni a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi kira ga tsige shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wani minista da yayi Magana kan sharadin boye sunansa a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba ya bayyana cewa basu aminta da tsarin shugabancinsa ba.

Gwamnonin APC na neman a tsige Oshiomhole

Gwamnonin APC na neman a tsige Oshiomhole
Source: Depositphotos

Ministan yayi ikirarin cewa gwamnonin basu bayar da komai bat a fannin kudi a babban taron jamiyyar sannan suna tu lura da yadda za’a yi da kudin da aka samu daga siyar da fam.

Ministan ya yi Karin haske cewa wasu gwamoni sun gana da shugaban kaasa Muhammadu Buhari don sanin yadda za’a bi a tsige Oshiomhole.

KU KARANTA KUMA: An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da za ta magance wadanda ke gujewa biyan haraji ta hanyar tserewa da kudadensu kasashen waje mai suna Voluntary Offshore Assets Regularization Scheme (VOARS).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel