An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami

An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami

- Jami'an tsaro sun saki shugaban DSS, Lawal Daura

- An kama shi ne bayan an sauke shi daga mukaminsa

- An tattaro cewa wasu na kusa da shi na kokarin ganin ya samu wani babban mukami a gwamnati

Rahotanni sun kawo cewa an saki tsohon shugaban hukumar yan sandan farin kaya, Lawal Daura.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an saki Daura ranar Talata, 9 ga watan Oktoba sannan kuma cewa wasu na kusa da shi na kokarin ganin ya samu wani babban mukami a gwamnati.

Wata majiya a fadar shugaban kasa a rahoto cewa na kusa da shi na kokarin ganin ya samu mukami mai muhimmanci a tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami

An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami
Source: Depositphotos

Wata majiya ta kuma bayyana cewa: “Wasu mambobin madafi da hukumomi masu karfi a gwamnati na ganin har yanzu ya kamata ace Daura ya samu muhimmin matsayi a kamfen din tazarcen Buhari.

“Wasu sun bayar da shawarar a daukeshi a matsayin kwararre d zai marawa kamfen din baya amma wasu na ganin yaa cancanci komawa matsayinsa a hukumar tsaro kamar yadda yake a 2015.

“Ina ganin zuwa yan makonni masu zuwa za’a shi matsayin da zai hau.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar Yansandan Najeriya ta garkame wani dan majalisan wakilai

Legit.ng ra rahoto a baya cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 13 ga watan Satumba ya bayyana Yusuf Magaji Bichi a matsayin sabon darakta janar na hukumar DSS.

Sabon shugaban ya karbi aiki ne daga hannun Mathew Seiyeifa, wanda ya maye gurbin Lawal Daura da aka kora.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel