Sojojin kasa sun ceto mutane sun kuma yi ram da wasu ‘Yan Boko Haram

Sojojin kasa sun ceto mutane sun kuma yi ram da wasu ‘Yan Boko Haram

Mun samu hotonan wasu ‘Yan Boko Haram da Sojojin Najeriya su ka kama a wata arangama da aka yi a cikin Jihar Borno. Rundunar Sojin kasar ne dai su ka fitar da wannan rahoto ba da dadewa ba.

Sojojin kasa sun ceto mutane sun kuma yi ram da wasu ‘Yan Boko Haram

Janar Buratai ya sarawa Sojoji bayan an ceto wasu kananan yara a Borno
Source: Facebook

Bataliyar Sojojin Najeriya na 22 na Garin Dikwa da ke Borno ta shiga sansanin ‘Yan ta’addan Boko Haram da ke Garin kaltunbare a cikin Jihar inda su ka damke wasu ‘Yan ta’addan yayin da su ka harbe wasu nan take.

Sojojin na Najeriya sun yi nasarar kama ‘Yan ta’adda wadanda su ka fitini Jama’a a Yankin. Wasu ‘Yan ta’addan sun yi kokarin tserewa yayin da su ka sha harbi daga hannun Jami’an Sojojin kasar na babban Bataliya ta 22.

KU KARANTA: Malamai sun shirya addu’ar kwana 40 don nema ma Buhari nasara

Shugaban hafsun Sojin kasar watau Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai ya yabawa Sojojin na sa da kan-sa inda ya nemi su cigaba da kokari wajen ganin an lallasa ‘Yan Boko Haram da su kayi saura a cikin kasar nan.

An dai yi nasarar ceto wasu yara 2 daga hannun ‘Yan ta’addan inda Shugaban Sojojin na Kasa ya jinjinawa Jami’an. Har yanzu dai ana fama da ragowar ‘Yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel