An cafke ma'aikatan hukumar NDLEA na bogi a jihar Kano

An cafke ma'aikatan hukumar NDLEA na bogi a jihar Kano

Mun samu cewa hukumar 'yan sanda ta jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu miyagun Mutane 4 da suka saba shiga da kuma basajar ma'aikatan hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA wajen cin Karen su ba bu babbaka.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Magaji Musa Majiya, shine ya bayar da shaidar hakan a jiya Laraba yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin na Kanon Dabo.

Yake cewa, wannan miyagu sun shafe lokuta masu tsayin gaske wajen cafke Mutane masu ta'ammali da muggan kwayoyi tare da tatse ma su dukiyoyin su cikin Birnin Kano da kewayensa.

Majiya ya bayar da sunayen Jami'an tsaron na bogi da suka hadar da; Tijjani Usman mazaunin unguwar Kurna, Muhammad Musa Haruna na unguwar Darmanawa, Adamu Usaman mazaunin unguwar Brigade da kuma Uzairu Bala na karamar hukumar Ungogo dake fadin birnin Kano.

An cafke ma'aikatan hukumar NDLEA na bogi a jihar Kano

An cafke ma'aikatan hukumar NDLEA na bogi a jihar Kano

Majia ya bayyana cewa, miyagun mutanen sun saba cin karen su ba bu babbaka tuburan a unguwannin Badawa, Hotoro, Mariri, Farawa, Bye Pass da kuma kasuwar Sabon Gari.

Bincike ya tabbatar da cewa, wannan miyagun mutane sun tatse dukiyoyin al'umma masu yawan gaske na miliyoyin Nairori yayin amsa laifin su, inda suka bayyana sunayen wasu Mutane 5 na daban da suke cikin wannan kungiya ta su da a halin yanzu an bazama cikin neman su.

KARANTA KUMA: Nasarar Atiku ba ta girgiza mu ba - Gwamnonin Jam'iyyar APC

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, hukumar za ta gurfanar da wannan miyagun mutane a gaban kuliya da zarar ta kammala binciken ta tare da kara kaimi wajen gudanar da bankado wasu miyagun masu makamancin wannan hali.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a jiya Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule tare da wasu gwamnoni biyar na jam'iyyar APC da kuma Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo a fadar Villa dake babban birnin nan kasar nan na Abuja.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel