Kungiyoyin kare hakkin biladama sun zargi Kwankwaso da shiryawa Ganduje tuggu

Kungiyoyin kare hakkin biladama sun zargi Kwankwaso da shiryawa Ganduje tuggu

Wasu kungiyoyin sa kai masu rajin kare hakkin biladama sun zargi tsohon gwamnan jahar Kano, kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso da shirya ma gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje kullalliya.

Kungiyoyin sun yi wannan batu ne game da wani bidiyo da ba’a kai ga saki ba dake nuna wani gwamnan daga jihohin arewacin Najeriya yana karbar makudan kudade da suka kai dala miliyan biyara a matsayin cin hanci daga yan kwangila, wanda rahoton jaridar Daily Nigerian ya nuna Gwamna Ganduje ne.

KU KARANTA: An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyoyin sun hada da Citizens for Justice Network, CJN, Peoples Alliance for Indigenous Rights, PAIR, Society for Civic and Gender Equity, SoCEGE, da Network for Transparency, NET, inda cikin wata sanarwar ta hadaka da suka fitar a ranar Laraba 10 ga watan Oktoba a garin Abuja, inda suka bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege, kamar yadda masu magana da yawunsu Isa Mahmud da Okoronkwo Chuks suka bayyana.

Isa da Chuks sun bayyana rahoton a matsayin wani lamari da aka shirya shi don cusa rudani a tsakar gidar jam’iyyar APC, inda suka ce babu yadda za’ayi ace wani mutum balle ma gwamna ya cusa kudin da suka kai dala miliyan biyar a aljihun wandonsa.

Kungiyoyin sun ce bayan dogon bincike, sun tabbatar da cewar wannan rahoto kadan ne daga cikin aikin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kungiyarsa ta Kwankwasiyya da basa ga maciji da Gwamna Ganduje, wanda suke son ganin sun kawo rudani a arewa maso yamma, inda shugaba Buhari ya fi yawan masoya.

“Maganar gaskiya shine mawallafin wannan rahoto na Daily Nigeria, Jaafar Jaafar tsohon kaakakin Kwankwaso ne, kuma yana aiki da shi har yanzu, duba da yadda ya sha kayi a kokarinsa na zama shugaban kasa, yanzu ya dawo yana iza rikicin siyasa a yankin Arewa maso yamma. Amma ya sani ba zai samu nasara ba.” Inji su.

Kungiyoyin sun yi mamakin yadda daga kallon bidiyo za’a gane adadin kudaden da wani mutumi ya sanya a aljihu, don haka suka ce yan Najeriya wayayyu ne, kuma ba zasu taba gamsuwa da irin wannan rahoton cin zarafi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel