Hadimar Buhari ta farkewa shugaban CAN laya a kan sukar shugaban kasa

Hadimar Buhari ta farkewa shugaban CAN laya a kan sukar shugaban kasa

Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren kafofin sada zumunta na zamani, Lauretta Onochi, ta rubuta wata budaddiyyar wasika, da ta wallafa a shafinta na Facebook, zuwa ga shugaban kungiyar kiristoci na kasa (CAN), Samson Olasupo.

Onichie ta fusata ne bayan shugaban kungiyar CAN din ya soki shugaba Buhari a kan rabon mukamai, in da ya zargi shugaban kasa da jirgewa a bangaren arewa a rabon mukamai.

Sai dai Onichie ta bayyana sukar ta sa da cewar cike ta ke da rashin sanin bayanai tare da kokarin bata sunan shugaba Buhari da gangan.

"Ni ban fahimci me shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista (CAN) zai karu da shi daga yawan sukar shugaban kasa ba.

"Kana ta fadawa jama'a karya a kan cewar nade-naden da shugaba Buhari da Osinbajo ke yi sun jirge ga bangare guda na Najeriya.

"Duk nade-naden da suke yi, suna yi ne bisa cancanta," a cewar Onichie.

Hadimar Buhari ta farkewa shugaban CAN laya a kan sukar shugaban kasa

Buhari da shugaban CAN
Source: Original

Mai taimakawa shugaban kasar ta zargi Olasupo da karbar kudi daga wasu 'yan adawa domin bata sunan shugaba Buhari.

A watan Satumba ne Olasupo ya zargi shugaba Buhari da bawa Arewa da musulmi fifiko a nade-naden mukaman gwamnatin tarayya tare da bayyana cewar nunawa mabiya addinin Kirista wariya na daga cikin abubuwan da ke kara tayar da hankula a kasa bakidaya.

DUBA WANNAN: Muna nan tafe zuwa gare ka: Albishir din EFCC ga daya daga attajiran Najeriya

Olasupo ya zargi Buhari da maye gurbin Matthew Seiyefa da Yusif Bichi, musulmi, maye gurbin ministar kudi Kemi Adeosun da Zainab Ahmed da kuma nadin Abbas Umar a matsayin shugaban hukumar dab'i ta kasa a matsayin wasu daga cikin irin rashin adalci da aka yiwa kiristoci.

Sai dai Onichie ta ce shugaban na CAN na nuna kiyayyarsa ne ga musulmi da kuma rashin sanin komai a kan kundin tsarin mulkin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel