Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

Mun samo daga The Cable cewar akwai wasu gwamonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ke numan tsige shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole.

Wannan bayanin ya fito daga bakin wani Minista ne da ya nemi sakayya sunansa yayin da ya yi hira da manema labarai a ranar Laraba.

Ministan ya ce wasu gwamnoni da ke fushi da Oshiomhole sunki bayar da gudunmawar kudi yayin da za'a gudanar da babban taron APC na da akayi a Abuja kuma a halin yanzu suna sanya idanu domin ganin yadda za'a kashe kudaden da aka samu daga sayar da fom din takara.

Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari

Wasu gwamnoni na neman tsige Oshiomhole - Ministan Buhari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo

"Wasu gwamnonin da basu gamsu da kamun ludayin Oshiomhole sun fadawa shugaba Buhari cewar dole a tsige Oshiomhole muddin ana son jam'iyyar APC tayi nasara a babban zaben 2019.

"Gwamnonin sun ce ba zasu iya aiki da Oshiomhole ba hakan yasa suka ki bayar da gudunmawa lokacin gudanar da babban taron jam'iyya na kasa inda suka bukaci Oshiomhole ya yi amfani da N10bn da ya tara wajen sayar da fom kuma suna sanya ido kan yadda zai kashe kudin," inji shi.

Ya kuma ce gwamnonin sun fara shirya dabarun yadda za a tsige Oshiomhole.

Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya fito fili ya cacaki Oshiomhole inda ya ce yana ji da kansa kamar wani karamin mahallici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel