Nasarar Atiku ba ta girgiza mu ba - Gwamnonin Jam'iyyar APC

Nasarar Atiku ba ta girgiza mu ba - Gwamnonin Jam'iyyar APC

Mun samu cewa a jiya Laraba gwamnonin jam'iyyar APC suka bayyana cewa, nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa ta lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP ba zai daga hankalin jam'iyyar su ba.

Gwamnonin sun bayyana cewa, ko kusa shugaban kasa Muhammadu Buhari ko jam'iyyar sa ta APC ba za su girgiza ba a sanadiyar nasarar Atiku a matsayin wanda zai rike tutar jam'iyyar PDP yayin zaben shugaban kasa a 2019.

Ko shakka ba bu Atiku shine wanda ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yayin zaben fidda gwani da aka gudanar can birnin Fatakwal na jihar Ribas a ranar Lahadin da ta gabata.

An zayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirrance da aka gudanar tare da shugaban kasa, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da kuma wasu gwamnoni 5 na jam'iyyar APC.

Nasarar Atiku ba ta girgiza mu ba - Gwamnonin Jam'iyyar APC

Nasarar Atiku ba ta girgiza mu ba - Gwamnonin Jam'iyyar APC
Source: Facebook

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, shine ya bayyana hakan tare da kyautata zato gami da sa ran nasarar jam'iyyar da cewa ba bu wanda zai lashe babban zabe na 2019 face shugaba Buhari.

KARANTA KUMA: Jam'iyyun Siyasa sun yiwa Mata rashin adalci yayin Zabukan Fidda Gwanaye - NCWS

Ya ci gaba da cewa, sabanin yadda ake ikirari a wasu sassa na kasar nan, nasarar Atiku a matsayin marikin tuta na jam'iyyar PDP ba za ta hana daga hankali ko girgiza jam'iyyar su ta APC.

Sauran wadanda suka halarci ganawar ta sirrance sun hadar da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, gwamnan jihar Bauchi; Muhammad Abubakar, gwamnan jihar Kano; Abdullahi Ganduje, Gwamnan jihar Borno; Kashim Shettima, gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode da kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel