Muna na zuwa gare ka - EFCC ta yiwa daya daga cikin attajiran Najeriya albisir

Muna na zuwa gare ka - EFCC ta yiwa daya daga cikin attajiran Najeriya albisir

- Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta ci al washin tabbatar da cewar ta kama shugaban kamfanin kera motocin Innoson, Chukwuma Innoson, tare da gurfanar da shi a gaban kotu

- EFCC ta yi wannan barazana ne yau, Laraba, bayan kotu ta soke tuhumar da hukumar ke yiwa Innoson saboda gaza kama shi tare da kawo shi gaban kotun da EFF ta yi

- EFCC na tuhumar Innoson tare da kamfaninsa da aikata laifuka hudu da suka hada da karya, zamba, sata da ha'inci

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ta ci al washin tabbatar da cewar ta kama shugaban kamfanin kera motocin Innoson, Chukwuma Innoson, tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

EFCC ta yi wannan barazana ne yau, Laraba, bayan kotu ta soke tuhumar da hukumar ke yiwa Innoson saboda gaza kama shi tare da kawo shi gaban kotun da EFF ta yi.

Alkalin kotun dake sauraron kararraki na musamman dake zamanta a Ikeja, jihar Legas, Jastis Olusola Williams, ya yi watsi da tuhumar almundahana da EFCC ke yiwa Innoson.

Muna na zuwa gare ka - EFCC ta yiwa daya daga cikin attajiran Najeriya albisir

Jami'an EFCC
Source: Depositphotos

Bayan wannan hukunci na kotun Legas ne, hedkwatar EFCC dake birnin tarayya, Abuja, ta bakin Wilson Uwujaren, kakakin hukumar, fitar da brazanar kama Innoson tare da gurfanar da shi.

EFCC na tuhumar Innoson tare da kamfaninsa da aikata laifuka hudu da suka hada da karya, zamba, sata da ha'inci.

Hukumar ta bayyana cewar wanda take zargin, Innoson, ya aikata wadannan laifuka ne a Leags tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011.

Ana zargin Innoson da gabatar da takardun bankin GT domin barin wasu sassan motoci da babura da ya sayo daga kasar China su shigo Najeriya da sunan cewar bankin ne ya bashi kwangilar da su.

A hukuncin da ya yanke a yau, Jastis Mojisola Dada, ya sanar da EFCC cewar alhakinsu ne su gabatar da shi a gaban kotun, idan kuma ba zasu iya ba, su hakura da shari'ar.

DUBA WANNAN: 'Yan sandan SARS sun kama dan majalisar wakilai na APC daga arewa

A baya, ranar 22 ga watan Yuni, 2018, Jastis Dada ya taba janyewa daga sauraron karar bisa shawar da hukumar kula da sashen shari'a (NJC) ta bayar.

A kwanakin baya ne Innoson ya bayar da kyautar wasu manyan motocin na alfarma ga shugaba Buhari domin a yi amfani da su wajen yakin neman zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel