Yunkurin kwace takara daga hannun surukinsa, Kwankwaso ya yi barazanar fita daga PDP

Yunkurin kwace takara daga hannun surukinsa, Kwankwaso ya yi barazanar fita daga PDP

Jim kadan bayan fadi a zaben fidda gwanin shugaban kasa a jam'iyyar PDP, da alamun tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakilta mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai sake ficewa daga jam'iyyar PDP.

Majiyar Daily Nigerian ta bayyana cewa an sami labarin sakon da Sanata Kwankwaso ya aikawa jam'iyyar PDP kan wata zama da aka shirya yi a yau kan canza dan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PDP.

Kwankwaso ya bayyana cewa shi fa ba zai halarci wannan zama ba kuma da zaran aka canza wadanda ya zaba domin takara a matakai daban-daban a jihar, zai koma jam'iyyar ADC.

Yunkurin kwace takara daga hannun surukinsa, Kwankwaso ya yi barazanar fita daga PDP

Yunkurin kwace takara daga hannun surukinsa, Kwankwaso ya yi barazanar fita daga PDP
Source: Facebook

KU KARANTA: Kotu ta soke dukkan 'yan takarar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Ribas

Mun kawo muku rahoton cewa Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP na shirin maye Abba Yusuf Kabir, da wani a matsayin dan takaran gwamnan jihar Kano a zaben 2019.

Jaridar Daily Nigerian ta tattaro cewa mataimakin shugaban jam'iyyar ta kasa bangaren Arewa maso yammacin Najeriya, Ibrahim Kazaure, ne ke kan gaba wajen wannan sabon shirin bisa ga zargin cewa zaben fidda gwanin da Yusuf Abba ya lashe akwai magudi.

Game da cewar majiya, kimanin deleget 50 da suka kunshi shugabannin jam'iyyar a kananan hukumomi da dattawan jamiyyar zasu hadu a Abuja yau Laraba domin zaben wanda suka ga ya cancanta da maye Abba Yusuf.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel