Ambaliyar ruwa ta shafe gonaki 500 na Shinkafa a jihar Bayelsa

Ambaliyar ruwa ta shafe gonaki 500 na Shinkafa a jihar Bayelsa

Mun samu rahoton cewa akwai akalla kimanin gonakin shinkafa 500 da suka salwanta a garuruwan Okpotuwari da Ondewari dake karamar hukumar Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa a sanadiyar aukuwar wata mummunar ambaliyar ruwa.

Kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban kungiyar manoman shinkafa na jihar, Mista Ezekiel Ogbianko, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba da ta gabace mu.

Mista Ogbianko yayin yawon shawagi da gani da ido a gonakin da ambaliyar ruwan ta cinye, ya kuma nemi gwamnatin tarayya da ta jiha akan ta kawo dauki na gaggawa ga manoman da annobar ta afkawa.

Ambaliyar ruwa ta shafe gonaki 500 na Shinkafa a jihar Bayelsa

Ambaliyar ruwa ta shafe gonaki 500 na Shinkafa a jihar Bayelsa
Source: Facebook

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan annoba ta ambaliyar ruwa tayi matukar muni sakamakon aukuwar ana daf da fara girbin amfanin gona.

KARANTA KUMA: Aukuwar wani mummunan hari na Boko Haram ta salwantar da Rayuka 48 a gabar Tafkin Chadi

A baya kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, akwai kimanin mutane 150, 000 da suka rasa muhallansu sanadiyar aukuwar ambaliyar ruwa a bana kadai cikin jihar ta Bayelsa.

Kazalika jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, sa'o'i kadan da suka gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri tare da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma wasu gwamnoni biyar na jam'iyyar APC a fadar Villa dake birnin Abuja.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel