Girma ya fadi: Ana zargin wani maigadi dan shekaru 55 da yiwa 'yar shekaru 10 fyade

Girma ya fadi: Ana zargin wani maigadi dan shekaru 55 da yiwa 'yar shekaru 10 fyade

Alkalin kotun Majistare da ke Minna ya bayar da umurnin garkame wani mai gadi mai shekaru 55, Michael Itang da ake zargi da yiwa wata yarinya mai shekaru 10 fyade.

Dan sandan mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwoche ya ce wata Grace Tanko da ke zaune a kusa Babban Asibitin Gwamnati da ke Suleja ne ta shigar da kara caji ofis na Suleja a ranar 3 ga watan Oktoba.

Ikwoche ya ce wanda ta shigar da karar ta yi ikirarin cewa Itang wanda ke gadi a Christ Revival Clinic a Suleja ya yiwa diyar ta mai shekaru 10 dabara ya shigar da ita dakinsa kuma ya rika lalata da ita lokuta daban-daban.

Wani shawarakin mai gadi ya yiwa wata yarinya fyade saboda N20

Wani shawarakin mai gadi ya yiwa wata yarinya fyade saboda N20
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Majalisa ta nada sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

A cewarsa, wanda ake zargin yana bawa yarinyar toshiyar baki na N20 zuwa N100 duk lokacin da zai yi lalata da ita.

Ya ce wannan laifin ya ci karo da sashi na 18 na dokar kare hakkin kananan yara na Jihar Neja ta shekarar 2010.

Sai dai bayan an karanto masa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, Itanga ya musanta aikata laifin.

Hakan yasa dan sanda mai shigar da karar ya bukaci kotu da dage cigaba da sauraron karar domin 'yan sandan su kammala bincikensu.

Alkalin kotun, Nasiru Muazu, ya bayar da umurnin a bawa Itang matsuguni a gidan yari kuma da daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel