Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC

Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC

- Oshiomhole ya maidawa INEC martani kan zaben fidda gwani na APC a jihar Zamfara da hukumar ta ce jam'iyyar bata gudanar ba

- INEC ta ce wakilanta na jihar Zamfara sun bata tabbacin cewa APC bata gudanar da zaben akan lokacin da ta kayyade ba

- Sai dai Oshiomhole ya ce an gudanar da zaben ne a ranar 6 zuwa 7 ga watan Oktoba a otel din City King da ke Gusau

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole ya maidawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC martani, yana mai bayyanawa karara cewa jam'iyyar ta gudanar da zabenfitar da gwani na kujerar gwamna, wakilan tarayya da kuma wakilan dokoki na jihar Zamfara kuma da su ne zata gudanar da zaben 2019.

Wannan martani na Oshiomhole ya zo ne awanni kadan bayan da sakataren riko na hukumar INEC, Okechukwu Ndeche ya fitar da wata sanarwa da ke cewar APC bata gudanar da zaben fitar da gwani a jihar Zamfara a tsakanin lokutan da hukumar ta kayyade ba. A cewar hakan, APC na iya rasa yan takara a zaben 2019 a jihar.

"Bisa rahotannin da muka samu daga wakilanmu na jihar Zamfara, sun tabbatar mana cewa babu wani zaben fitar da gwani da APCta gudanar a jiahr, bisa kundin doka na hukumar zabe 2010, sashe na 87 da na 31, jam'iyyar APC ba zata iya gabatar da 'yan takara a zaben 2019 a jihar Zamfara ba," a cewar sanarwar INEC.

KARANTA WANNAN: Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba

Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC

Zaben 2019: APC na da 'yan takara a jihar Zamfara - Martanin Oshiomhole ga INEC
Source: Depositphotos

Sai dai a martanin da ya mayarwa INEC awanni kadan da wannan sanarwa, Oshiomhole ya karyata wannan wasika ta INEC na cewar jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba.

"Muna so kowa ya sani cewa babu wata hanya da za'a iya bullo da ita don wargaza gaskiyar abubuwan da suka faru a jihar Zamfara."

Da ya ke hada hujjojin rahoton kwamitin gudanar da zaben jam'iyyar a jihar Zamfara tare da wannan martani nasa, Oshiomhole ya ce an gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar ne a ranar 6 zuwa 7 ga watan Oktoba a otel din City King da ke Gusau, kuma 'yan takar sun samu nasara ne ta hanyar wakilta dan takara kai tsaye ba tare da wani zabe ba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel