Jam’iyyar APC ta karyata INEC na cewa ba ta da ‘Yan takara a 2019

Jam’iyyar APC ta karyata INEC na cewa ba ta da ‘Yan takara a 2019

Mun samu labari dazu nan cewa Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki Adams Oshimhole ya maidawa Hukumar zabe na kasa watau INEC martani na cewa ba ayi zaben fitar da 'Dan takara a Jihar Zamfara ba.

Jam’iyyar APC ta musanya INEC na cewa ba ta da ‘Yan takara a 2019

Bangaren wasikar da Shugaban Jam’iyyar APC ya aikawa INEC
Source: UGC

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya aika takarda zuwa ga Mukaddashin Sakataren Hukumar zaben na INEC watau Okechukwu Ndeche inda ya bada amsar wasikar da ya aiko masa game da rashin ‘Yan takaran APC a Jihar Zamfara.

Adams Oshiomhole ya bayyana cewa APC tana da ‘Yan takarar ta na zaben 2019 kuma Jam’iyyar za ta aiko da sunayen su kafin wa’adin da Hukumar ta bada ya kure. A Ranar 18 ga wannan Watan ne dai INEC za ta daina karbar sunayen ‘Yan takara.

Shugaban APC yace Hukumar INEC tayi hanzarin daukar matakin cewa APC ba ta da ‘Yan takara a zabe mai zuwa. Oshiomhole yace an shirya zaben fitar da gwani a Jam’iyyar a Zamfara kuma da zarar an ci ma matsaya za a aikowa INEC sunayen su.

KU KARANTA: APC ba ta da ‘Yan takara a Jihar Zamfara a zaben 2019 - Inji PDP

Kwamared Oshiomhole ya nuna rashin jin dadin sa na yadda INEC ta dauki wannan mataki tun kafin ta ji daga bakin Jam’iyyar duk da cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ba ta gudanar da zabe ba a Jihar Kano kuma Hukumar zaben ba ta aika mata takarda ba.

Jam’iyyar APC dai ta hakikance kan cewa za tayi takara a zabe mai zuwa. Oshimohole ya nuna cewa da zarar sun samu maslaha a cikin Jam’iyyar za a ga sunayen ‘Yan takarar Majalisar Jiha da ta Wakilai da Dattawa da ma ‘Dan takarar Gwamna a Zamfara.

Jiya kun ji cewa Abdulaziz Yari ya lashe tikitin Sanata a Jam’iyyar APC a zaben da shugaban APC na Zamfara wanda Uwar Jam’iyya ta kora watau Lawali M. Liman ya gudanar cikin tsakiyar dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel