Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba

Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba

- Wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar da umurnin cafke Adam Oshiomhole tare da gurfanar da shi saboda zarginsa da aikata zamba

- Bishop Osodolor Ochei ne ya gabatarwa kotun wannan bukata, wanda ya zargi Oshiomhole da karkatar da wasu kudaden jiha zuwa aljihunsa

- Lauyan Bishop Ochei ya tabbatar wa kotun cewa akwai kwararan hujjoji da suka hada da hotuna da zasu tabbatar da cewa Oshiomhole ya zambaci jihar Edo

Wata babbar kotu da ke da zama a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da umurnin kakkabe wasu takardun kara da aka gabatar a gabanta da suka bayyana bukatar umurtar hukumar EFCC da ta cafke shugaban jam'iyyar APC na kasa Adam Oshiomhole tare da gurfanar da shi saboda zarginsa da aikata zamba.

Mai shari'a Anwuli Chikere ya bayar da wannan umurni a ranar Talata a bayan karanta wata takardar bukatar tuhuma da wani mai rajin dakile cin hanci da rasha, Bishop Osodolor Ochei ya gabatarwa kotun, wanda ya zargi Oshiomhole da karkatar da wasu kudaden jiha zuwa aljihunsa.

KARANTA WANNAN: An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

Mai shari'a Chikere, a yayin da yake baiwa hukumar EFCC wannan umurni na bincikar shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce itama EFCC zata bi tsarin gudanar da binciken kotun, yana mai cewa za a gudanar da binciken ne cikin kwanaki 5 daga 9 ga watan Oktoba, 2018, ranar da umurnin ya fara aiki.

Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba

Kotu ta amince da tuhumar shugaban APC na kasa Adam Oshiomhole bisa zargin aikata Zamba
Source: Twitter

Takardar buktar tuhumar mai dauke da lambar shigar da kara FHC/ABJ/628/2018, wacce Bishop Osodolor Ochei ya gabatar ta hannun lauyansa, Dr. West Idahosa, ta sanya Oshiomhole a matsayin wanda take kara tare da sanya EFCC a matsayin hukumar da take so ta gudanar da binciken tuhumar.

KARANTA WANNAN: Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa

Dr. Idahosa, da yake kare wannan kudiri a gaban kotun, ya bukaci kotun da ta baiwa wadanda za a yi shari'ar da su damar maida nasu martanin kan wannan zargi da ake yi masu, musamman ganin cewa wanda ya shigar da karar ya mara baya ne ga yunkurin gwamnatin tarayya na yaki da cin hanci da rashawa.

A ranar 28 ga watan Oktoba, 2016, Bishop OChie ya shigar da EFCC kara kan Oshiomhole wanda ya ke a matsayin gwamnan jihar Edo daga watan Nuwambar 2008 zuwa 11 ga watan Nuwambar 2016.

Dr. Idahosa, a rokon da ya yiwa kotu na amincewa da wannan bukata ta tuhumar Oshiomhole, ya kuma ce akwai bayanai da zasu zamo kwararan hujjoji, da suka hada da hotunan gidajen alfarma na tsohon gwamnan, wadanda gaba daya rayuwar shi bai taba mallakar kudin da zai saye su da kuma hujjar yadda Oshiomhole ya karkatar da kudin wani aiki da gwamnatin Edo ta waje zuwa nashi aikin na kashin kasa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel