Kotu ta soke dukkan 'yan takarar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Ribas

Kotu ta soke dukkan 'yan takarar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Ribas

Jastis Chiwendu Nwogu na wata babbar kotu dake zamanta a Fatakwal, jihar Ribas, ya soke zaben Tonye Cole a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ribas a karkashin jam'iyyar APC.

Da yake yanke hukuncin a yau, Laraba, jastis Nwogu ya bayyana cewar zaben Cole a matsayin dan takarar APC cike yake da karya doka da saba ka'ida.

Kazalika kotun ta soke dukkan 'yan takarar kujerar Sanata, majalisar wakilai da na dokokin jihar.

Kotun ba ta tsaya iya nan ba sai da ta kara da yanke hukuncin rushe dukkan shugabannin mazabu, kananan da na jiha da aka zaba a taron gangamin APC a jihar. Kotun ta ce ta rushe su ne saboda taron gangamin da ya samar da su ba a yi shi bisa ka'ida ba.

Jastis Nwogu ya kara da cewar, duk wanda ya sayi fam din takara neman shugabanci a jam'iyyar APC na ikon shiga zaben da aka yi ranar 19 ga watan Mayu, 2018, amma sai aka yiwa wasu rashin adalci ta hanyar hana su shiga zaben.

Kotu ta soke dukkan 'yan takarar da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Ribas

Ofishin jam'iyyar APC a jihar Ribas
Source: Twitter

"Dole kotu ta zama gatan maras gata, ba zai yiwu a yiwa doka karan tsaye kotu ta bari ba," a kalaman jastis Nwogu.

Tun bayan kammala zabukan shugabannin mazabu, kananan hukumomi da matakin jiha a Ribas, Ibrahim Imah da wasu mutane 22 suka shigar da kara kotu bisa zargin saba dokokin jam'iyyar APC a zabukan da aka gudanar.

DUBA WANNAN: Bayan ganawa da Obasanjo, Afenifere ta fadi dan takarar da zata goyawa baya

Duk da wani tsagi na jam'iyyar ta APC ya garzaya Abuja tare da shigar da wata kara na neman a hana kowacce kotu yin hukunci a kan batun zabukan, jastis Nwogu ya ce hakan ba zai hana shi yanke hukunci ba tunda karar dake gabansa aka shigar wa.

Wannan hukunci na Jastis Nwogu ya rushe dukkan wasu 'yan takara da jam'iyyar APC ke tunanin tana da su a jihar Ribas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel