Takarar Atiku: Gwamnatin Tarayya na sake kokarin ta ki Ikweremadu kurkuku kafin Atiku ya kira shi

Takarar Atiku: Gwamnatin Tarayya na sake kokarin ta ki Ikweremadu kurkuku kafin Atiku ya kira shi

- Gwamnatin tarayya ta maka Sanata Ike Ekweremadu da Sanata Bassey kotu

- Tana zargin su da kin bayyana dukiyar su

- Gwamnatin tarayya na binciken dukiyoyin yan siyasa domin kwato dukiyoyin da aka handame

Takarar Atiku: Gwamnatin Tarayya na sake kokarin ta ki Ikweremadu kurkuku kafin Atiku ya kira shi

Takarar Atiku: Gwamnatin Tarayya na sake kokarin ta ki Ikweremadu kurkuku kafin Atiku ya kira shi
Source: Depositphotos

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu da Sanata Bassey Akpan, mai wakiltar arewa maso gabas na jihar na gaban kuliya sakamakon kin bayyana dukiyar su da sukayi ga kwamiti na musamman na kwato dukiyar kasa da mahandama suka kwashe.

Majiyar mu tace ana zargin su da laifi biyu a ranar 10 ga watan Octoba a gaban mai shari'a John tsoho na babban kotun tarayya dake Abuja.

Kotun ta umarci da a bayyana ma mahukuntan laifukansu a rubuce ta hannun kilakin majalisar dattawa.

DUBA WANNAN: Sanatocin APC da PDP na aiki tare don cire Saraki

Mai shari'a ya maida 22 ga watan Octoba domin sauraron shari'ar Ekweremadu, shi kuma Sanata Akpan zuwa 19 ga watan Nuwamba.

A yayin haka ne, a ranar 10 ga watan Octoba, shugaban majalisar ya rantsar da Sanata Lawal Gumuau daga kudancin Bauchi da Sanata Ahmed Baba Kaita da arewacin Katsina.

An rantsar da Sanatocin a washegarin da aka bude majalisar bayan dogon hutun da tayi.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel