Majalisa ta saka baki kan batun neman Janar Alkali da aka tsinci motarsa a Jos

Majalisa ta saka baki kan batun neman Janar Alkali da aka tsinci motarsa a Jos

- Majalisar Dattawa ta bukaci hukumomin tsaro su binciko Janar Akali da sauran mutanen da suka bace a Jos

- Majalisar kuma da bukaci gwamnatin ta kafa kwamitin bincike domin gano dalilin da yasa mutanen jihar suka ki amincewa a bincika kududufin da farko

A yau, Laraba ne Majalisar Wakilai ta yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen neman Janar Muhammed Alkali da sauran 'yan Najeriya da aka gano kayayakinsu a wata kududufi da ke Dura-Du ta jihar Plateau.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincike domin dalilin da yasa mutane garin Dura-Du suka rika jefa motoccin mutane a cikin kududufi.

Majalisa ta saka baki kan batun neman Janar Alkali da aka tsinci motarsa a Jos

Majalisa ta saka baki kan batun neman Janar Alkali da aka tsinci motarsa a Jos
Source: Depositphotos

An bayar da sanarwar bacewar Mr Alkali ne a ranar 3 ga watan Satumban 2018 a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga babban birnin tarayya Abuja.

DUBA WANNAN: Na yi matukar mamakin yadda Atiku ya zama dan takarar PDP - Obasanjo

Makonni kadan bayan bacewarsa ne Hukumar Sojin Najeriya ta samu bayyanan sirri cewar akwai yiwuwar gawar Janar din da motarsa suna cikin wani kududufi da ke Dura-Du sai dai da farko mutanen garin basu amince a bincika kududfin ba.

Matan garin sunyi zanga-zangar hana sojin gudanar da binciken amma hakan bai yi nasara ba kuma daga baya an gano motar Janar Alkali dauke da rigarsa, takalminsa da wasu tufafinsa a ranar 3 ga watan Oktoba.

Daga baya an sake gano wasu motocci guda biyu cikin kududufin ciki har da bus din fasinjoji ama har yanzu ba'a gano gawarwakin wadanda ke cikin motar da shi Janar din ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel