Zanga-zanga: Nakasassu sun toshe hanyar shiga majalisar dokokin kasar

Zanga-zanga: Nakasassu sun toshe hanyar shiga majalisar dokokin kasar

Wani rahoto daga Channels Television ya nuna cewa wasu nakasassun mutane a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba su mamaye kofar shiga majalisar dokokin kasar cikin zanga-zanga.

A cewar rahoton, masu zanga-zangan na bukatar majalisar dokoki ta mika dokar kare nakasassu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya sanya hannu.

Dokar nakasassu shine wanda majalisun dokokin kasar biyu suka gabatar domin kare ýancin ýan Najeriya dake da nakasa.

Zanga-zanga: Nakasassu sun toshe hanyar shiga majalisar dokokin kasar

Zanga-zanga: Nakasassu sun toshe hanyar shiga majalisar dokokin kasar
Source: Facebook

Dokar kuma yana bukatar a daina nuna kiyayya ga nakasassu da kuma basu hakkinsu na zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari da Osinbajo na ganawa da gwamnonin APC 5

A wani lamari na daban, mun ji cewa Yan majalisar wakilai na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun sanar da nadin Idris Wase daga jihar Plateau a matsayin mataimakin shugaba a majalisar.

Wase, wanda ya maye gurbin marigayi Umar Jibrin da ya rasu a watan Afrilun wannan shekarar bayan fama da rashin lafiya ya karbi rantsuwar aiki ne a yau Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel