Aukuwar wani mummunan hari na Boko Haram ta salwantar da Rayuka 48 a gabar Tafkin Chadi

Aukuwar wani mummunan hari na Boko Haram ta salwantar da Rayuka 48 a gabar Tafkin Chadi

Mun samu cewa kimanin rayukan Shahidai 48 ne suka salwanta yayin wani mummunan hari na kungiyar ta'adda ta Boko Haram da ya auku ranar Larabar da ta gabata a gabar Tafkin Chadi kamar yadda wani kakakin dakarun soji ya bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito wannan rahoto da ta kalato daga kafar watsa labarai ta AFP ta bayyana cewa, rayuka 48 da suka salwanta sun hadar da dakarun soji 8 na kasar Chadi.

Rayuka 48 sun salwanta yayin wani hari na Boko Haram a gabar Tafkin Chadi

Rayuka 48 sun salwanta yayin wani hari na Boko Haram a gabar Tafkin Chadi
Source: UGC

A yayin ci gaba da bayanansa ga manema labarai, Kakakin sojin ya bayyana cewa wannan lamari ya auku ne a yayin da dakarun sojin ke kokarin mayar da martani ga famarkin na 'yan ta'adda.

Ya ci gaba da cewa, harin ya auku ne da sanyin safiyar ranar ta Laraba a wani sansanin dakaru na Kaiga Kindji dake gabar tafkin Chadin.

KARANTA KUMA: Dattijo 'dan shekara 55 ya murkushe Yarinya 'yar shekara 10 a jihar Neja

Legit.ng ta fahimci cewa, ba ya ga salwantar wannan adadi na rayukan Mutane, akwai kuma dakarun soji suka jikkata yayin aukuwar harin kamar yadda jaridar ta AFP ta ruwaito.

Kazalika jaridar ta kuma ruwaito cewa, wasu Sanatocin jam'iyyar APC da PDP za su hada kai da juna wajen tsige shugaban majalisar dattawa daga kujerar sa, Abubakar Bukola Saraki da mataimakin sa, Ike Ekweremadu.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel