EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn

EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn

- EFCC ta kafa kwamiti na musamman da zai yi bincike kan badakalar N1.2bn da ake zargin Sambo Dasuki ya baiwa gwamna Ayodele Fayose a 2014

- Mai magana da yawun gwamna Fayose, ya ce mai gidan nasa a shirye yake ya fuskanci wannan tuhuma ta EFCC

- Sai dai a bangare daya, tuni Fayose ya shigar da EFCC kotu na sanya jami'an tsaro su cafke shi da zaran yayi yunkurin barin kasar

Hukumar da aka kafa don bincike kan laifukan ta'addanci da kudaden gwamnati da kuma yaki da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa, EFCC ta kafa wani kwamiti na musamman da zai yi bincike kan Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti a mako mai zuwa kan zarginsa da almundahana, jaridar Punch zataniya tabbatar da labarin.

Fayose, wanda ya kasance a saman kujerar gwamna tun 16 ga watan Oktoba, 2014, zai rasa madafun iko da misalin karfe 11.59 na daren ranar 15 ga watan Oktoba, 2018, wanda hakan zai baiwa hukumar EFCC cikakken ikon cafke shi, tsare shi da kuma yanke masa hukunci.

Ana sa ran gwamnan zai gurfana a babban ofishin hukumar ta EFCC da ke Abuja don ganawa da daraktan ayyuka na hukumar, Umar Mohammed, wanda daga bisani ne za a hsda shi da kwamiti na musamman da zai fara gudanar da bincike akansa.

KARANTA WANNAN: An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn

EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn
Source: Depositphotos

Fayose dai ana tsaka mai wuya tare da fuskantar tuhuma kan zarginsa da ake yi na karbar N1.2bn daga tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta fuskar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya), ta hannun tsohon ministan cikinngida kan tsaro, Sanata Musiliu Obanikoro.

Ana zargin cewa an baiwa Fayose ajiyar kudinnnr a lokacin da ake yakin zaben gwamnan jihar a 2014 da ya gudana a jihar ta Ekiti. Banda wannan kuma akwai zargin sa da handame kudin kwantiragi.

Da yake jawabi ga jaridar Punch a ranar Talata, mai magana da yawun Fayose, Mr. Idowu Adelusi, ya ce mai gidan nasa a shirye yake na fuskantar EFCC. Adelusi ya bayyana cewa tuni dama gwamnan ya aikewa hukumar da wasikar nuna hadin kai na gurfana a gabanta a mako mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki

EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn

EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn
Source: Depositphotos

Sai dai a wani labarin, Fayose ya shigar da karar hukumar EFCC tare da neman tarar N20bn sakamakon makala masa masu sanya ido a dukkanin harkokinsa, da kuma baiwa jami'an tsaro umirnin cafke shi da zaran yayi yunkurin barin kasar.

Ya ce wannan umurnin na EFCC ya saba dokar kundin tsarin kasa kasancewar har yanzu yana saman karagar shugabancin jihar, don haka yana da cikakkiyar kariya daga duk wata tuhuma, har sai ya sauka.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel