Yanzu Yanzu: Buhari da Osinbajo na ganawa da gwamnonin APC 5

Yanzu Yanzu: Buhari da Osinbajo na ganawa da gwamnonin APC 5

A yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cikin ganawa tare da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) guda biyar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Hadimin shugaban kasa a shafukan zumunta, Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba a shafinsa na twitter.

A cikin ganawar harda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Gwamnonin jihohin da ake ganawar dasu sun hada da na Kano, Borno, Bauchi, Imo da Lagos.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai

Ga yadda ya rubuta a shafin nasa:

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na cikin ganawa da gwamnonin Kano, Borno, Bauchi, Imo da Lagos a fadar shugaban kasa, Abuja.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel