Abinda Nuhu Ribadu ya rattaba wa Obasanjo kan Atiku Abubakar bayan binciken PTDF da EFCC tayi

Abinda Nuhu Ribadu ya rattaba wa Obasanjo kan Atiku Abubakar bayan binciken PTDF da EFCC tayi

- EFCC ta sami Atiku da laifin amfani da karfin Ofishinsa don arzurta kansa

- Anyi kasuwanci da kudin gwamnati, miliyoyin daloli

- Mukarraban Atikun sun amfana daga badakalar

Abinda Nuhu Ribadu ya rattaba wa Obasanjo kan Atiku Abubakar bayan binciken PTDF da EFCC tayi

Abinda Nuhu Ribadu ya rattaba wa Obasanjo kan Atiku Abubakar bayan binciken PTDF da EFCC tayi
Source: Twitter

Koda yake, a halin yanzu ba'a ji gwamnati na neman bin diddigin ta'inda su Bola Tinubu suka sami kudi ba, wadanda ke neman kujera lamba daya, tasu kuras tayi kuka, inda ake ta zaqulo yadda har Atiku ya zama biloniya daga aikin gwamnati.

Rahoton EFCC a 2016, wanda Nuhu Ribadu ya jagoranta, a lokacin ana kokarin hana Atiku yin takarar PDP, ya same shi da laifin amfani da kudaden gwamnati ba bisa qa'ida ba.

EFCC ta rattaba wa Obasanjo bayanai kamar haka, bayan da aka kalli daya daga cikin ofisoshi da yake shugabanta a matsayinsa na mataimakin shugaba.

DUBA WANNAN: Buhari zai sake ciwo bashi na biliyoyin daloli

A PTDF, kudaden mai da ake tarawa don koyawa 'yan Najeriya yadda ake aikin mai da ma daukar nauyin atisayen aikin, an samu Atikun yayi babakere kan rarraba wasu kudade bankuna, inda su kuma bankunan, sukan baiwa abokansa (yaransa) bashin kudi daga lalitarsu, don a ci riba biyu.

Ribadu na son Obasanjo ya:

1. Kwace Ofishin PTDF daga hannun Atiku/Ofishinsa

2. A kwato kudade da abokai da yaransa da ma bankuna suka amfana dasu

3. A kai kotu, a tuhumi, Yusuf Hamisu Abubakar, shugaban PTDF, da sauran na hannun daman Atikun, kamar su Otumba Fasawe.

4. A kwato kudaden gwamnati da bankuna suka sanya a kamfanin Globacom na waya, wanda suma daga wannan kudaden PTDF aka samo su.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel