Babu wani da zai iya mana dauki-dora irin na Tinubu a jiharmu - gwamnan arewa

Babu wani da zai iya mana dauki-dora irin na Tinubu a jiharmu - gwamnan arewa

- Gwamna Samuel Ortom yace siyasar ubangida da tayi aiki a Legas bata da matsuguni a Benue

- Yace Akume ya dame shi ba zai saboda baya aiki ba, sai saboda yaki amincewa a juya shi

- Ya kuma zargi Akume da waskar da Naira biliyan 2 daga kudin jihar lokacin da yake mulki

Babu wani da zai iya mana dauki-dora irin na Tinubu a jiharmu - gwamnan arewa

Babu wani da zai iya mana dauki-dora irin na Tinubu a jiharmu - gwamnan arewa
Source: Depositphotos

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya sanar da Sanata George Ortom cewa siyasar ubangida da akeyi a jihar Legas ba zatayi tasiri a jihar Benue ba.

Ortom yace Akume ya takura mishi ne ba don rashin aiki ga jihar ba, sai saboda kin yin biyayya gareshi.

Ya kuma zargi Akume da waskar da Naira biliyan 2 na jihar a yayin da yake gwamnan jihar gurin cika burin shi na zama Sanata a 2007.

Ortom, wanda yayi maganar ta bakin mai bashi shawara ta musamman akan yada labarai, Tahav Agerzua, a yayin da yake maida martanin cewa da akayi Ortom bai tsinana abin azo a gani a ofishin shi ba.

DUBA WANNAN: Rahoton EFCC kan Atiku a 2006

A taron manema labarai da Akume yayi a gidanshi dake Makurdi, ya zargi cewa sama da Naira biliyan 500 da aka samu a mulkin Ortom baiyi abin azo a gani dashi.

Tsohon gwamnan ya tausayawa ma'aikatan jihar na cewa gwamnan ya hana su albashi. Ya bai wa mutanen jihar Benue hakuri saboda shi ya kawo Ortom a 2015.

Mataimakin gwamnan yace kalubantar Ortom da tsohon gwamnan yakeyi ba don komai bane sai saboda yaki biyayya tare da amincewa ya juya shi.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel