Rikici na ci gaba da yin gaba a APC yayinda Gwamna Yari ke shirin maka jam’iyyar a kotu kan zaben fidda gwani

Rikici na ci gaba da yin gaba a APC yayinda Gwamna Yari ke shirin maka jam’iyyar a kotu kan zaben fidda gwani

- Rikici na ci gaba da barkewa a jamiyyar APC mai mulki reshen Zamfara

- Gwamna Yari na shirin maka jamiyyar a kotu

- Hakan na faruwa ne sanadiyar kin amincewa da sakamakon zaben fidda gwani na gwamna a jihar

Rikici ya barke a jamiyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki yayinda Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ke shirin maka jam'iyyar a kotu kan kin amincewa da sakamakon zaben fidda gwani a jihar.

An rahoto cewa Yari yayi fushi akan sakamakon zaben fidda gwani wanda aka gudanar a jihar da ya haddasa tashin hankali.

Rikici na ci gaba da yin gaba a APC yayinda Gwamna Yari ke shirin maka jam’iyyar a kotu kan zaben fidda gwani

Rikici na ci gaba da yin gaba a APC yayinda Gwamna Yari ke shirin maka jam’iyyar a kotu kan zaben fidda gwani
Source: Depositphotos

Daily Trust ya ruwaito cewa kwamitin zaben karkashin jagorancin Abubakar A Fari sun soke zaben fidda gwani akan hanya sakamakon rikici da barazanar da aka yiwa masu zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai

Don haka daga bisani wani sakamako ya billo daga kwamitin masu ruwa da tsaki na jamiyyar wanda ya kai ga dakatar da shugabannin jam’iyyar a jihar.

Wata majiya kusa da gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana tattaunawa akan shirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel