Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN

- Majalisar dattawa ta tabbatar da Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON

- Ta kuma tabbatar da Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN

- Hakan na zuwa ne kwana daya bayan ta dawo daga dogon hutun da ta tafi

Majalisar dattawa a ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba ta tabbatar da Muiz Banire tsohon mai ba jam’iyyar All Progressives Congress shawara akan doka, a matsayin shugaban hukumar kula da dukiyoyi na maaikatun Najeriya.

Majalisar ta kuma tabbatar da Folasdodun Adebisi Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin Najerya.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan CBN
Source: UGC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya zabi Shonubi a ranar Juma’a 8 ga watan Yuni a wata sanarwa daga kakakin shugaban kasar, Garba Shehu.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya rantsar da sabbin sanatoci 2

An nada Banire wanda ya kasance babban lauyen Najeriya (SAN) a ranar Talata, 17 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel