An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

A yanzu haka hukumomin tsaro a Najeriya sun dukufa wajen gudanar da bincike akan wasu faya fayan bidyo da suka samu wadanda ke nuna gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje dumu dumu yan karbar makudan kudade da suka kai dala miliyan 5 ($5, 000, 000), kimanin naira biliyan daya da miliyan dari takwas (N1, 800, 000, 000) kenan a matsayin cin hanci.

Jaridar Daily Nigerian ce ta gudanar da wannan bincike cikin natsuwa, tsanaki da takatsantsan don tabbatar da gaskiyar wannan bidiyon domin gudun kada ace sharri ko kazafi ake yi ma wanda fuskarsa ta bayyana a cikin bidiyon tare da muryarsa.

KU KARANTA: An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

Ganduje
Source: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan kwangiloli da dama dake gudanar da manyan ayyuka daban daban a jahar Kano sun tabbatar da cewa gwamna Ganduje da kansa ne yake karbar kashi goma sha biyar zuwa kashi ashirin da biyar na kudaden kwangilar da gwamnatin jahar ke basu.

Kuma zuwa yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci wasu hukumomin tsaro su kai masa rahoton abinda suka binciko game da wannan bidiyo da cikin gaggawa don daukan matakin daya dace da wannan gwamnan.

Rahoton da shugaba Buhari ya nema ya hada da binciken muryar dake aka jiyo a cikin bidiyon, tabbata da gaskiyar hotunan bidiyon da kuma tsare tsaren bidiyon, sa’annan su baiwa Buhari shawara kan matakin daya dace ya dauka.

“Buhari ya kalli bidiyon farko ne a wani babban talabijin dake ofishinsa, gaskiya bai ji dadin kallon wannan bidiyon ba, yayi bakin ciki matuka, na san zai dauk matakin daya kamata.” Inji majiyar.

A cikin wadannan bidiyon guda uku an hangi gwamnan tana karbar kudaden da suka kai dala miliyan biyar a ranaku daban daban, an hangi gwamnan a cikin wani bidiyon ya fito ba ko hula akansa yana daukan sunayen yan kwangilan da suka kawo kudin, sa’annan ya zuba bandir na daloli a aljihunan rigansa da na wandonsa.

A wani bidiyon kuma an hangi gwamnan ya karbi cin hancin dala miliyan uku ya jefa su a cikin aljihun malum malum da ya sanya, da wannan ne majiyar Legit.ng ta gayyatao kwararru akan harkar bidiyo don tabbatar da gaskiyar bidiyon, inda suka tabbatar da cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ne.

“Binciken kwakwaf da muka yi ya tabbatar mana da hotunan sun yi daidai da hotunan gwamnan, kuma muryar da ake ji a bidiyon muryar gwamnan ne.” Inji wani kwararre da ya duba bidiyon. Daga karshe majiyarmu ta yi alkawarin wallafa bidiyon nan bada jimawa ba.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar a yanzu haka an fara kullekullen tsige wannan gwamna, musamman idan shugaban kasa ya mika bukatar tsigeshi ga majalisar dokokin jahar, ana ganin ba zasu yi wata wata ba wajen tsige shin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel