Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai

Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya rantsar da wani sabon mamba na majalisar wakilai, Haruna Isah wanda aka zaba kwanakin baya a zaben cike gurbi na mazabar Lokoja/Koton-Karfe dake jihar Kogi.

An rantsar da Harunar a yau Laraba, 10 ga watan Oktoba kwana daya da dawowar majalisar daga dogon htun da ta tafi.

Ya lashe zaben cike gurbi wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar don cike kujerar Umar Jibrin wanda ya rasu a ranar 30 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai

Yanzu Yanzu: Dogara ya rantsar da sabon mamba a majalisar wakilai
Source: UGC

Mista Isah ya samu kuri’u 26,860 inda ya kayar da abokin takaransa na jam’iyyar Democratic Party (PDP), Bashir Abubakar wanda ya samu kuri’u 14, 845.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya rantsar da sabbin sanatoci 2

Marigayi Jibrin ya kasance mataimakin kakakin majalisar wakilai kafin mutuwarsa.

Marigayin ya kasance dan jam’iyyar APC mai mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel