Karin kudin albashi: Gwamnati N24,000 zata iya biya, amma kungiyar kwadago ta tubure kan N30,000 - Ngige

Karin kudin albashi: Gwamnati N24,000 zata iya biya, amma kungiyar kwadago ta tubure kan N30,000 - Ngige

Gwamnatin tarayya ta alanta cewa bayan shawarwari da tattaunawa, ta gabatar da N24,000 a matsayin sabon kudin albashin ma'aikatan gwamnati.

Ministan kwadago da daukan aiki, Chris Ngige ya bayyana hakan ne a yau Laraba yayinda yake hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwan tarayya FEC.

Mr Ngige ya laburta hakan ne bisa ga rahotanni da ya sami cewa shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Ayuba Wabba, ya sanarwa jama'a cewa kwamitin sunyi ittifaki kan kara kudi albashi daga 19,200 zuwa N30,000.

Ngige ya ce wannan batu ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Ministoci 25 sun halarci zaman majalisar zartarwa da Buhari ya jagoranta

A cewarsa, yayinda kwamitin suka zauna ranan 5 ga watan Oktoba bayan janye yajin aiki, kungiyoyin kwadago sun sauko N30,000 yayinda saura ma'aikatu suka yarda a N25,000.

Ya kara da cewa bayan ganawar, sun tattauna da gwamnoni Najeriya gaba daya inda aka ajiye magana cewa za'a biya ma'aikatan gwamnatin tarayya N24,000 sannan ma'aikatan jiha, N20,000.

Ngige ya karashe da cewa game da dokan kungiyoyin kwadago na duniya, abu mafi muhimmanci kan karin albashi shine a iya biya.

Gabanin yanzu, kungiyar kwadagon Najeriya ta bukac gwamnati ta kara kudin albashi daga N18,000 zuwa N50,000 alal akalli, amma gwamnonin jihohi sun nuna rashin amincewarsu da wannan abu.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel