Ministoci 25 sun halarci zaman majalisar zartarwa da Buhari ya jagoranta

Ministoci 25 sun halarci zaman majalisar zartarwa da Buhari ya jagoranta

Akalla ministoci ashirin da biyar ne suka halarci zaman majalisar zartarwa da ake sati sati a fadar shugaban kasa wanda ya kunshi kafatanin ministocin Najeriya da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar, tare da wasu manyan hadiman shugaban kasa.

Da yake ba’a yi wannan zama ba a satin daya gabata saboda zabukan fidda gwani na jam’iyyar APC da suka gudana inda aka zabi yan takarkarun jam’iyyara a matakin mukamai daban daban, daga ciki har da wata ministan Buhari, Zainab Bukar Abba.

KU KARANTA: Kasafin kudin 2018: Buhari ya saki naira biliyan 300 don gudanar da manyan ayyuka

Ministoci 25 sun halarci zaman majalisar zartarwa da Buhari ya jagoranta

Shittu
Source: UGC

Sai dai a zaman na yau an hangi keyar ministan sadarwa, Adebayo Shittu, wanda uwar jam’iyyar APC ta haramta masa shiga takarar gwamnan jahar Oyo sakamakon rashin yin aikin bautan kasa na NYSC a bayan ya kammala karatun jami’a.

Da yake karin haske dangane da haramta ma Shittu shiga sahun yan takarar da zasu fafata a zaben fidda gwani na APC a takarar gwamnan jahar Oyo, shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole ya bai gamsu da uzurin da Shittu ya bayar ba na cewa wai yayi bautan kasa a majalisar dokokin jahar Oyo.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 10:56 na safiyar Laraba ne Shittu ya isa fadar shugaban kasa sanye da kaftani baka da hula akansa, inda ya shiga dakin taron yana bin kujera kujera yana gaisawa da takwarorinsa da aka kwana biyu ba’a sadu ba.

A daidai lokacin da za;a fara wannan zama ne sai shugaba Buhari ya umarci ministan watsa labaru, Alhaji Lai Muhammed da ya bude taro da addu’ar musulunci, yayin da ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ya bude da na kiristanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel