Kasafin kudin 2018: Buhari ya saki naira biliyan 300 don gudanar da manyan ayyuka

Kasafin kudin 2018: Buhari ya saki naira biliyan 300 don gudanar da manyan ayyuka

Ministan kasafin kudi da na tsare tsare, Udoma Udo Udoma ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta saki kui naira biliyan dari uku domin cigaba da manyan ayyukan dake cikin kasafin kudin shekarar 2018, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan ya bayyana haka ne a yayin taron cibiyar lamuni ta duniya, IMF da na bankin duniya, inda yace ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai karu da kashi 2.1 zuwa karshen shekarar 2018.

KU KARANTA: Siyasar 2019: Wani Malamin addini ya dukufa saukar Qur’ani a kullum don samun nasarar Atiku

Kasafin kudin 2018: Buhari ya saki naira biliyan 3000 don gudanar da manyan ayyuka

Ministan
Source: Depositphotos

“Muna tsammanin zuwa karshen shekarar 2018 zamu kara girma da kashi 2.1, ba yadda muke so ba kenan, amma muna kokarin gyara abubuwa da dama, mun fi karfi a yanzu fiye da shekarar 2015, kudadenmu na asusun kasar waje sun kai dala biliyan 44.

“Kuma muna da riba a kasuwanci, tunda dai abubuwan da muke shigo dasu basa karuwa, amma abubuwan da muke fitarwa na karuwa fiye da a baya, duk wasu alkalumma sun nuna muna tafiy yadda ya kamata.” Inji shi.

Ita ma a na ta jawabin, ministar kudi, Ahmed Zainab ta bayyana cewa a yanzu haka tattaunawa ta yi nisa tsakanin gwamnati da bankin shiga da fitar da kayayyan nahiyar Afirka game da burinsa na gina cibiyar kiwon lafiya a Abuja.

“Haka zalika muna tattaunawa da wasu manyan kamfanoni dake son hadin gwiwa da ma’aikatan kasuwanci da zuba jari ta Najeriya a wajen gina cibiyoyin zuba jari guda uku a Lekki na jahar Legas, Kano da Kaduna.” Inji ta.

Sai dai a nasa jawabin, shugban bankin shiga da fitar da kayayyan nahiyar Afirka, Benedict Oromah ya bayyana cewa Najeriya ta sauka daga matsayinta na ta daya a tsakanin kasashen nahiyar Afirka dake rike da kaso mai tsoka na jarin bankin, inda yace kasar Misra ce ta daya a yanzu, sai Zimbabwe, sai Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel