Hasashe: mutane 10 da Atiku zai iya zaba matsayin mataimakinsa a 2019

Hasashe: mutane 10 da Atiku zai iya zaba matsayin mataimakinsa a 2019

Bayan samun nasaran Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin Peoples Democratic Party (PDP), an fara farautan wanda zai zama mataimakinsa.

Wanda jam’iyyar PDP ta zaba matsayin dan takara na da matukar muhimmanci ga nasarar samun tunbuke shugaba Buhari daga mulki a 2019.

Hukumar INEC ta baiwa jam’iyyun siyasa dama kawo sunayen yan takaransu da mataimakansu zuwa ranan 18 ga watan Oktoba 2018.

Zuwa yanzu, rahotannin sun bayyana cewa za’a zabi mataimakin Atiku cikin yankin kudu maso yamma ko kudu maso gabashin Najeriya. Yayinda yankin inyamurai ke ganin hakkinsu ne a basu kujeran, jam’iyyar PDP na ganin baiwa yankin Yarbawa zai fi.

KU KARANTA: 2019: Mutane 32 da za suyi takara da shugaba Muhammadu Buhari

Ga jerin wadanda ake ganin za’a zaba:

1. Dr Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kudin Najeriya zamanin Obasanjo, Yar’adua da Goodluck Jonathan.

2. Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu: Lauya kuma dan siyasa wanda ya kasance mataimakin shugaban majalisar dattawa karo na uku yanzu.

3. Sanata Enyinnaya Abaribe: Sanata a jihar Abiya wanda ya tsayawa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

4. Peter Obi: Tsohon gwamnan jihar Anambara wanda ya mulki jihar sau biyu kafin mikawa gwamnan Obiano

5. Nyesom Wike: Gwamnan jihar Ribas, kuma tsohon ministan ilimi karkashin gwamnatin Jonathan

6. Charles Soludo: Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN

7. Chike Obi

8. Akinwumi Adesina: Shugaban kasa bankin cigaban Afirka kuma tsohon ministan aikin noma

9. Gbenga Daniel: Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma diraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar

10. Jimi Agbaje: Dan takaran kujeran gwamnan jihar Legas

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel