Yanzu Yanzu: Wani jigon PDP ya yanke jiki ya fadi a kotu

Yanzu Yanzu: Wani jigon PDP ya yanke jiki ya fadi a kotu

Wani jigon jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Osun, Fatai Oyedele, wanda aka fi sani da Diekola ya yanke jiki ya fadi a kotu.

An gurfanar da Diekola, Segun Adekilekun da kuma Sikiru Lawal a gaban kotu a yau Laraba, 10 ga watan OKtoba bayan yan sanda sun kama su kafin sake zaben gwamna da akayi a ranar 27 ga watan Satumba, jaridar The Punch ta ruwaito.

Amma bayan an kira wadanda ake zargin sun fito gaban kotu, sai Diekola wanda ke manned a filasta a hannunsa ya yanke jiki ya fadi,inda sauran masu laifin suka yi gaggawan taimaka masa.

Yanzu Yanzu: Wani jigon PDP ya yanke jiki ya fadi a kotu

Yanzu Yanzu: Wani jigon PDP ya yanke jiki ya fadi a kotu
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa an bawa Diekola wanda aka ce ya nuna alamu na tsananin rashin lafiya kujerar zama sannan alkalin kotun majistare, Olusegun Ayilara ya bayyan cewa ba zai iya shari’ar mutumin dake rai a hannun Allah ba.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 2 da ya zama dole Atiku ya yi la’akari da su kafin zabar abokin tafiya – Shugabannin PDP

Ya dage zaman zuwa ranar 23 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraron shari’an.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel