2019: Tikitin takara ya tarwatsa jam’iyyar APC a Niger

2019: Tikitin takara ya tarwatsa jam’iyyar APC a Niger

- Tikitin takara na barazanar tarwatsa jam’iyyar APC a jihar Niger

- Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da APC ta kulla da wasu ýaan majalisun tarayya na dawo dasu majalisar dokokin kasar

- Sanatocin jihar guda uku duk sun fadi zaben fidda gwani

Yarjejeniyar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kulla da wasu ýaan majalisun tarayya na dawo dasu majalisar dokokin kasar na barazana ga zaman lafiya a jam’iyyar babin jihar Niger.

Bincike ya nuna cewa domin hana sanatoci da ýan majalisar wakilai sauya sheka irin wanda ya afku a kwanakin baya, shugaban jam’iyya ya kulla yarjejeniya da wasu ýan majalisa inda ya basu tabbacin dawo masu da tikitin su.

201: Tikitin takara ya tarwatsa jam’iyyar APC a Niger

201: Tikitin takara ya tarwatsa jam’iyyar APC a Niger
Source: Depositphotos

Tuni yarjejeniyar ya samu cikas a babin jam’iyyar na jihar Niger, yayinda wasu yan takaran suka ki amincewa da Sanata Divid Umoru, Sabe Abdullahi, Mustapha Sani a matsayin wadanda aka tsayar da yankuna uku na jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya rantsar da sabbin sanatoci 2

Da suke jawabi a taron manema labarai a Abuja a ranar Talata, 9 ga watan Oktoba, Alhaji Muhammed Sani Musa, Muhammed Birma da Alhaji Zakari Jika Toro, sun fadama manema labarai cewa sune suka lashe tikitin jam’iyyar kuma sun sha alwashin daukar mataki na hana tursasa wa yankunansu sanatoci masu ci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel