Muhimman abubuwa 2 da ya zama dole Atiku ya yi la’akari da su kafin zabar abokin tafiya – Shugabannin PDP

Muhimman abubuwa 2 da ya zama dole Atiku ya yi la’akari da su kafin zabar abokin tafiya – Shugabannin PDP

Shugaban jamiyyar Peoples Democratic party (PDP), Uche Secondus ya gana dad an takarar kujerar shugaban kasa na jamiyyar a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar.

Secondus tare da sauran shugabannin jam'iyyar sun shiga ganawa da Atiku domin yanke shawara kan wanda zai zamo abokin takararsa a zaben 2019.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ganawar ya gudana ne a ofishin kamfen din PDP, Lagacy House a babban birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa Atiku da tawagarsa ne suka fara isa wajen taron amma sai da suka jira Secondus da tawagarsa, wanda suka samu jinkiri a jirginsu da ya taso daga Port Harcourt.

Muhimman abubuwa 2 da ya zama dole Atiku ya yi la’akari da su kafin zabar abokin tafiya – Shugabannin PDP

Muhimman abubuwa 2 da ya zama dole Atiku ya yi la’akari da su kafin zabar abokin tafiya – Shugabannin PDP
Source: Twitter

Majiyoyi sun bayyana cewa a taron wanda ya kwashe tsawon sa’o’i biyu, jam’iyyar ta nemi Atiku ya gabatar da sunayen wadanda yake so a matsayin abokin tafiya domin jam’iyyar ta tattauna tare da shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago sun rufe ayyuka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed

An kuma tattaro cewa jam’iyyar ta gindaya masa wasu sharuda da zai bi wajen zabar abokin takara da zasu kara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Sharudan sune:

1. Abokin takarar ya kasance ya fi Atiku karancin shekaru

2. Ya kuma kasance mai ilimin tattalin arziki sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel