Karshen alewa: Hadaddiyar kungiyar yarbawa ta fara kunyata Tinubu

Karshen alewa: Hadaddiyar kungiyar yarbawa ta fara kunyata Tinubu

Hadaddiyar kungiyar nan ta 'yan kabilar yarbawa dake da'awar kare hakkin su da mutuncin su a Najeriya mai suna Afenifere ta yi fata-fata da tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta Afenifere tana tsokaci ne akan kalaman da jigon na APC yayi game da takaddamar da ake fama da ita a kasar ta tsakanin fulani da manoma akan wuraren kiwo.

Karshen alewa: Hadaddiyar kungiyar yarbawa ta fara kunyata Tinubu

Karshen alewa: Hadaddiyar kungiyar yarbawa ta fara kunyata Tinubu
Source: Facebook

KU KARANTA: Yadda kymarar boye ta fallasa wani gwamna yana ansar cin hanci

Legit.ng ta samu cewa shi dai Tinubu a nashi ra'ayin ya bayyana cewa rashin wuraren kiwo na musamman ruwan sha ne ummul-haba'isin tashe-tashen hankulan da fulani ke haddasawa don haka ne ma ya shawarci cewa gwamnati tayi kokarin samar da su don makiyayan.

Sai dai su kuma a nasu ra'ayin, kungiyar ta Afenifere ta bayyana hakan a matsayin abun ta kaici inda tace shi Tinubun ya bata kunya da irin wannan shawarar ta sa domin a cewar su, hakan tunani ne irin na mutanen da.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari a jiya ya roki malaman addinai a Najeriya da su taimaka ma gwamnatin sa wajen ganin ta yi nasa a yakin da take yi da 'yan ta'addan dake boyewa cikin rigar addini.

Shugaban kasar yayi wannan roko ne a lokacin da ya karbin bakuncin shugabannin kungiyar Qdiriyya ta Afrika a karkashin jagorancin shugaban ta Sheikh Qribullah Nasiru Kabara a fadar sa dake a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel