Shugaba Buhari ya nemi taimako da goyon bayan malaman addinai

Shugaba Buhari ya nemi taimako da goyon bayan malaman addinai

Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari a jiya ya roki malaman addinai a Najeriya da su taimaka ma gwamnatin sa wajen ganin ta yi nasa a yakin da take yi da 'yan ta'addan dake boyewa cikin rigar addini.

Shugaban kasar yayi wannan roko ne a lokacin da ya karbin bakuncin shugabannin kungiyar Qdiriyya ta Afrika a karkashin jagorancin shugaban ta Sheikh Qribullah Nasiru Kabara a fadar sa dake a garin Abuja.

Shugaba Buhari ya nemi taimako da goyon bayan malaman addinai

Shugaba Buhari ya nemi taimako da goyon bayan malaman addinai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Kamanceceniya 5 tsakanin Buhari da Atiku

Legit.ng ta samu cewa shugaban kasar ya kara da cewa dole ne sai malaman sun tashi tsaye sun taimakawa gwamnati wajen yakar masu boyewa a cikin rigar addini suna juya kwakwalen 'yan kasar domin yin ta'addanci da kashe-kashe.

Tun farko dai da yake nasa jawabin, madugun 'yan darikar ta Qadiriyya, ya taya shugaban kasar murnan sake lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam'iyyar sa ta APC na zaben 2019.

A wani labarin kuma, Hadaddiyar kungiyar nan ta 'yan kabilar yarbawa dake da'awar kare hakkin su da mutuncin su a Najeriya mai suna Afenifere ta yi fata-fata da tsohon gwamnan jihar Legas, kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar ta Afenifere tana tsokaci ne akan kalaman da jigon na APC yayi game da takaddamar da ake fama da ita a kasar ta tsakanin fulani da manoma akan wuraren kiwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel