Ka tara kudi ta haramtaciyyar hanya – Kungiyar kamfen din Buhari ga Atiku

Ka tara kudi ta haramtaciyyar hanya – Kungiyar kamfen din Buhari ga Atiku

Daraktan kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mista Festus Keyamo (SAN), yace dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa,. Atiku Abubakar ya tara dukiyarsa ne ta haramtaciyar hanya da kuma damfara.

Keyamo ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, jaridar Punch ta ruwaito.

Yace Atiku na ta kasuwanci na kashin kansa a matsayinsaa na jamin kwastam wanda ya saba ma dokokin aikin gwamnati.

Ka tara kudi ta haramtaciyyar hanya – Kungiyar kamfen din Buhari ga Atiku

Ka tara kudi ta haramtaciyyar hanya – Kungiyar kamfen din Buhari ga Atiku
Source: Depositphotos

Babban lauyan yace kasuwancin Atiku wanda aka san yayi nasara ya kasance Integrated Logistics Services Nigeria Limited wanda aka fi sani da INTEL ne kawai.

Yace jami’ar Atiku na aiki ne kan kudin gwamnati. Sannan ya kalubalanci Atiku da ya kare kansa cewa kudin da aka yi amfani dashi wajen kafa makarantar ba na gwamnati bane.

Ya kuma kara da cewa nasarorin da aka samu a gwamnatin Obasanjo da Atiku ba wani abun al’ajabi bane.

KU KARANTA KUMA: Ba za mu tsige Dogara ba – Babban jigon APC

Cewa habbaka da aka samu ta fannin sadarwa abune day a faru a kusan dukkanin kasashen Afrika a waccen lokacin.

Keyamo yace koda dai Buhari bai da kudi kamar na abokin adawarsa, shugaban kasar ya nuna cewa ya fahimci yadda ake tafiyar da tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel