Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago sun rufe ayyuka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago sun rufe ayyuka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed

Rahotanni sun kawo cewa a safiyar yau Laraba, 10 ga watan Oktoba wasu kungiyoyin hukumar jirgin sama, sunyi tattaki a filin jirgin sama na Murtala Mohammed International Airport kuma sun rufe filin jirgin wanda aka fi sani da MM2.

Bisa ga rahotanni mambobin kungiyar sun rufe MM2 a kokarinsu na zanga-zanga kan sallamar wasu ma’aikatan da suka shiga kungiyoyin.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa daruruwan fasinjoji na nan kara zube yayinda masu zanga-zangar suka tsayar da ayyuka cak a filin jirgin saman Murtala Muhammed din.

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago sun rufe ayyuka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed

Yanzu Yanzu: Kungiyar kwadago sun rufe ayyuka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed
Source: Depositphotos

Kungiyoyin sunyi zanga-zanga kan zargin cewa BASL sun salami ma’aikata 20 da suka nuna ra’ayin shiga kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya nada kwamiti domin duba dalilin da ya sa Buhari yayi watsi da kudirin su

Kungiyoyin dake zanga-zangan sune National Union of Air Transport Employees (NUATE), Air Transport Services Senior Staff Association of Nigeria (ATSSSAN) da kuma National Association of Aircraft Pilots and Engineers (NAAPE).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel